1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na nazarin sassauta tarnakin corona

Abdullahi Tanko Bala
April 14, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na nazarin sassauta tarnaki kan zirga zirgar jama'a yayin da gwamnatinta ke shirin yanke shawara kan mataki na gaba na yaki da cutar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3atB2
02.02.2020, Berlin, Deutschland - Symbolfoto zum Thema Corona-Virus.
Hoto: Imago/R. Zensen

Cibiyar binciken kimiyya da yaki da cutattuka masu yaduwa ta Jamus ta bada shawarar sassauta tarnakin harkokin jama'a a kasar sakamakon raguwar yaduwar cutar coronavirus a fadin tarayyar Jamus.

Shugaban cibiyar Robert Koch ta yaki da cutattuka Farfesa Lothar Wieler ya ce gwamnati na iya bude makarantu a lokaci guda kuma a cigaba da sa ido kan matakan tsabatar muhalli.

"Yace bayananmu sun nuna ba a sami karuwar mutane da yawa da suka kamu da cutar a tsawon lokaci wanda hakan ke nufin cewa matakan da ake dauka suna yin tasiri kuma wannan labari ne mai kyau".

Bugu da kari ya ce ana iya bude shagunan sayar da kayayyaki da wuraren cin abinci idan aka cigaba da sa ido da martaba matakan tazara a tsakanin jama'a

Sai dai kuma yace akwai bukatar gwamnati ta bullo da dokar amfani da kyalen rufe baki da hanci ga al'umma idan suka fita bainar jama'a.