Kwalara ta kashe mutane 20 a Zimbabuwe
September 11, 2018An samu mutuwar mutane 20 sakamakon barkewar cutar Kwalara a kasar Zimbabwe a babban birnin Harare inda sama da mutane 2,000 suka kamu da ciwon sakamakon shan wani gurbataccen ruwa da suka yi.
Ministan lafiya na kasar Zimbabuwe Obadiah Moyo ya bayyana hakan a ranar Talata. Mahukuntan na birnin Harare dai sun dauki shekaru da dama amma sun gaza wajen samar da wadataccen ruwa mai tsafta ga al'umma, lamarin da ya sanya al'umma suke dogara da shan ruwa daga rijiyoyi budaddu da rijiyoyin burtsatse da al'umma ke samar wa kansu.
A shekarar 2008 dai kasar ta Zimbabuwe ta ga bala'in annobar cutar ta Kwalara lokacin da al'umma suka fada yanayi na matsalar tattalin arziki, an kuma samu mutane 4,000 da suka rasu baya ga 40,000 da suka harbu da kwayoyin cutar.