1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makarantu sama 700 ne dai aka rufe sakamamkon bullar cutar

Yusuf BalaJune 4, 2015

Makarantu sama 700 ne dai aka rufe sakamamkon bullar cutar. A ranar 20 ga watan Mayu aka sami wani mutum dan shekaru 68 da haihuwa ya kamu da cutar bayan ziyarar kasar Saudiyya.

https://p.dw.com/p/1Fba2
Südkorea Über 680 Menschen unter Quarantäne
Al'ummar Koriya ta Kudu na daukar matakan kariya daga MERSHoto: Reuters/K. Ju-sung

Darururuwan makarantu ne a ka rufe a kasar Koriya ta Kudu a ranar Alhamis din nan yayin da jami'an kasar suka himmatu wajen rage fargaba da dimuwa da al'umma suka tsinci kansu bayan barkewar kwayoyin cutar MERS mai alaka da numfashi, inda tuni aka samu mutane 35 sun harbu da kwayoyin wannan cuta, biyu kuma sun rasu saboda ita, abin da ya jawo soke shirin zirga-zirgar jirage da sauran ababan hawa.

Fiye da makarantu 700 ne aka rufe tun daga matakin makarantun rainon kanan yara zuwa kwalejojin ilimi, tun bayan barkewar wannan cuta a kasar bayan kasar Saudiyya.

A cewar ma'aikatar lafiya ta kasar Koriya ta Kudu a ranar Alhamis din nan an kara samun mutane biyar da suka kamu da cutar, abin da ya sanya adadadin wadanda suka kamu ya kai mutane 35.

A karon farko dai, da aka samu wannan cuta ta MERS mai nasaba da nimfashi, na zama ranar 20 ga watan Mayu inda aka sami wani mutum dan shekaru 68 da haihuwa ya kamu da cutar bayan ya dawo daga kasar Saudiyya.

Tun daga wancan lokaci ne aka kebe mutane kimanin 1,660 da ake zargin sun yi alaka da masu cutar dan yin nazari ko sun harbu da kwayoyin ta.