1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Neman magance cutar Noma a kasashen Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe Gudrun Heise/SB/LMJ
January 30, 2024

Cutar noma na farawa ne da kumburi kafin ta bazu ko'ina a fuskar wanda ya kamu da ita. Tana shafar lebe da fuska da hanci. Hasali ma, yawancin sassan fuska na lalacewa cikin 'yan kwanaki kalilan.

https://p.dw.com/p/4bqKu
Najeriya | Wadda ta tsira daga cutar Noma
Wadda ta tsira daga cutar NomaHoto: Fabrice Caterini/Inediz/MSF

Yau ne 30 ga watan Janairu, kasashe ke raya ranar duniya ta cututtukan da ake sako-sako da su a wurare da ake zafi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da cutar noma da ke lalata baki da fuska da kasusuwa ke dada yaduwa a Afirka. Har yanzu masu kamuwa da cutar na mutuwa cikin kankanin lokaci Ba tare da magani ba idan ba a dauki matakan gaggawa ba.

Karin Bayani: Hanyoyin inganta lafiya a Afirka

Amina mai shekara 18 na dHanyoyin inganta lafiya a Afirkaaga cikin wadanda suk kamu da cutar noma, kuma labarinta, wani bangare ne na shirin yaki da cutar noma da kungiyar agajin ta Medecins sans Frontières ta shirya tare da hadin gwiwar masu shirya fina-finan na kasar Faransa.

Najeriya | Mai fama da cutar Noma
Mai fama da cutar NomaHoto: Fabrice Caterini/Inediz/MSF

Masu bincike kan cutar noma sun nunar da cewar rashin abinci mai gina jiki da rashin tsaftar baki ne suke raunana tsarin garkuwar jiki, wanda ke sa kwayoyin cuta samun wurin zama. Sannan cututtuka da suka hada da kyanda ko zazzabin cizon sauro suna tasiri a kan tsarin rigakafi. Amma ba a yi bincike ba tukuna kan ainihin abubuwan da ke haifar da ita da kuma yadda cutar noma ke bayyana da habaka ba.

A yanzu, an samu ‘yar karamar nasara a yaki da muguwar cutar noma: Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanya noma cikin jerin cututtukan da aka yi watsi da su a wurare masu zafi. Wannan zai ba ta karin hankali da kuma albarkatun kudi da za a iya sanyawa a fannin bincike da kuma rigakafi.

Cutar noma ta yadu a kasashen Afirka, kuma Najeriya ce ta fi fama da matsalar inda take yaduwa a tsakanin yara 'yan kasa da shekaru bakwai. Akwai kusan yara 140,000 kowace shekara da suke kamuwa da noma, kuma kusan kashi 90% na mutuwa a cikin makonni biyu na farko matikar ba a shawo kan cutar da antibiotic ba. Yara da ke fama da cutar na tsoron zuwa makaranta sabowa wariya da ake nuna musu. Amma a mafi yawancin lokuta, iyaye ne ke boye su don nisantar da su daga idanun jama'a, ma'ana suna zama saniyar ware.

Najeriya | Mai fama da cutar Noma
Aiki kan cutar NomaHoto: Fabrice Caterini/Inediz/MSF

Amma al'amura sun sha banban a asibitin noma da ke Sokoto a Najeriya inji ma'aikaciyar jinya 'yar kasar Jamus Fabia Casti ta kungiyar agaji ta medecins sans frontières, wacce ta kula da marasa lafiyar noma na tsawon watanni tara. Masu fama da  cutar noma na shafe makonni hudu zuwa shida wajen shan magani a asibiti. Amma bayan haka, yawancin su na jira shekara daya zuwa biyu kafin a sanya sunansu cikin jerin wadanda za a yi aiki don yi musu gyaran fuska, a cewar Fabia casti

Yawancinsu masu fama da noma na fuskantar matsala wajen ci da sha da yin magana saboda cutar ta lalata fuskokinsu. Kwararrun likitocin tiyata suna kokarin gyara musu bangarorin fuskokinsu da suka lalace, duk da sarkakiyar da ke tattare da wannan aiki, lamarin da ke ba su damar komawa cikin 'yan uwa da dangi domin yin mu'amala rayuwa ta yau da kullun.