1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Zika ta bulla a kasar Amirka

Gazali Abdou TasawaFebruary 3, 2016

Hukumomin kiwon lafiya a Amirka sun tabbatar a jiya Talata da bullar cutar Zika a kasar inda suka ce an samu wani mutun guda da ya kamu da cutar nau'in da ake kamuwa ta hanyar jima'i

https://p.dw.com/p/1HoPD
Brasilien - Maßnahmen gegen Zika Virus - Rio de Janeiro
Hoto: Reuters/P. Olivares

Hukumomin kiwon lafiya a Amirka sun tabbatar a jiya Talata da bullar cutar Zika a kasar inda aka samu wani mutun guda da ya kamu da cutar nau'in wanda ake kamuwa ta hanyar jima'i. Lamarin da ya kara fargabar da ake da ita a game da bazuwar da cutar ke yi a duniya .

Tuni ma dai aka kira zuwa shirya wani taron gaggawa na ministocin kiwon lafiya na kasashen Kudancin Amirka a wannan Laraba a kasar Yurugai domin auna girman matsalar da daukar matakan taka mata birki.

Kungiyar Agajin Kasa da Kasa ta Redikuros ta yi shelar samar da taimakon gaggawa a yaki da cutar wacce ta fi hadari ga mata masu juna biyu, da kuma ta soma yaduwa tamkar wutar daji a kasashen duniya inda yanzu haka ko baya ga kasashen nahiyar Afirka da na Asiya ta bayyana a yankin latin Amirka musamman a kasar Brazil inda adadin yara da aka haifa da nakasar karamin kai da cutar Zikar ke haddasawa ya karu da kusan kashi 50 cikin dari a cikin mako daya kawai