1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da alamun cimma yarjejeniya a taron Beijing kan shirin nukiliyar Koriya Ta Arewa

February 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuSB
An shirya komawa kan teburin shawarawari a karshen makon nan da nufin kawo karshen shirin nukiliyar kasar KTA. An dai ga alamun samun wani ci-gaba bayan bayyana wani sabon shiri da zumar shawo kan gwamnati a Pyongyang ta yi watsi da shirin ta na nukiliya. To sai dai mahalarta taron na takatsatsan a daidai lokacin da suke shirye shiryen komawa ga shawarwari a birnin Beijing don aiki kan wata shawara da zata bukaci KTA ta takaita shirin ta na nukiliya. Wata majiya diplomasiya ta ce daftarin shawarar wadda China ta tsara ta yi nuni da cewa gwamnatin KTA zata dakatar tare da rufe tashar nukiliya ta Yongbyon a cikin watanni 2 kana a saka mata da taimakon makamashi da na tattalin arziki. To amma wakilin KTA Kye Gwam ya ce har yanzu akwai bambamce bambamcen ra´ayi akan wasu jerin batutuwa.