1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon birkin mota da zai rage haddura

Ramatu Garba Baba
February 12, 2019

Kasashen duniya 40 ne suka cimma matsaya kan soma amfani da wani sabon nau'in birkin mota da zai taimaka wajen takaita afkuwar haddura a tituna. Kasashen sun hada da Japan da kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/3DFET
Rosco McGlashan Rekord Geschwindigkeit
Hoto: AFP/Getty Images

Kasashen sun amince da lallai a sanya wannan nau'in birkin a cikin sababbin motoci da za a kera nan gaba da kuma wasu rukunin motocin haya da za a soma fitarwa a badi don amfanin jama'a.

 Alkaluma na wadannan kasashen da suka cimma matsaya, na nuni da cewa an sami aukuwar hadduran mota sama da 9,000 a shekarar 2016. Kasashen na ganin yin hakan riga kafi ne da ka iya taimakawa wajen kawar da haddura na ba gaira ba dalili a sanadiyyar rashin dace da matuka ke yi wajen sanya birki. Amirka da Chaina da Indiya dai, sun kauracewa wannan yarjejeniyar.