Dabbobin dajin Afirka: Hadari mai suna mutum
Kungiyoyin kare muhalli sun yi gargadi kan bacewar wasu halitttu, mutane ma suna cikin wannan barazanar. A albarkacin taron Majalisar Dinkin Duniya kan halittu na COP15 mun duba namun dajin Afirka.
Mai dogon wuya
Rakumin-dawa yana son rayuwa a Savannah, amma mazauna yankin na shafar rayuwarsu. Wannan dabba na cikin jerin lissafin da suke fuskantar barazana a cewar hukumar kula da inganta yanayi ta duniya a shekara ta 2021. Bazaranar bacewa saboda yadda ake kara mayar da Savannah wuraren kiwo da hakar ma'adanai. Yanzu an yi imanin kasa da rakumin-dawa 100,000 suka rage.
Masu jikekken hanci
Wannan biri ne da ake samu a Madagaska da ke zama tsibiri a gabashin Afirka. Duk nau'ikan an bayyana a matsayin suna cikin hadari. Kasa da guda 1000 suka rage a raye a cikin daji, musamman sun fi fita da dare.
Mai ado da digo
Mai gudu kamar iska - wannan shi ne taken damisa. Yana da basirar neman abinci. Suna iya gudun kilomita 95 cikin dakika uku kacal. Sune dabbobi da suka fi gudu a duniya. Amma mutane masu farauta sun jefa rayuwar damisa cikin barazana, inda kullum yawansu ke raguwa.
Zaki na jin yunwa: Ina abinci?
Kashe zakuna da yadda suke raguwa ya zama abin damuwa ga sarkin daji. Akwai lokacin da suke sarautar Savannah, a cewar asusun kula da halittu ta duniya, yanayin ya sauya. A yammacin Afirka akwai zakuna kasa da 500, na ahiyar baki daya akwai zakuna 20,000. Galibi da aka kebe a gandun daji na kasashe.
Cikin daji
Duk nau'ikan goggo guda hudu suna cikin dabbobin da ke cikin hadari. Yanzu kuma ga hadarin karuwar zafi sakamakon sauyin yanayi da muhalli da ya samu kansa. Amma masu farauta ta barauniyar hanya da cutar Ebola sun rage yawan dabbobin.
Saboda neman kaho
Karkanda na cikin dabbobi da suka dade a doron kasa. Suna cikin hadari, bakaken karkanda musamman suna fuskantar barazanar bacewa saboda masu farauta ta barauniyar hanya suna cire kahon - amma su kan kashe dabbar. Tun bayan kashe na karshe, abin da ya rage shi ne wadda aka haifa ta hanyar zuba kwayoyin halitta.
Hadari mai tsawo
Akwai karancin kunkuru a teku - akwai nau'ikan kunkuru bakwai da suka rage a duniya. A baya sun mamaye teku, sun tsallake lokacin da manyan kadangaru suka bace, sun kuma tsallake bala'o'i masu yawa. Wayar da aka samu ya zama abokin gaba da su. Suna cikin hadari musamman idan sauran dabbobi suka je bakin teku yin kwai. Kana ba za su iya bambanta dagolon da aka zubar a teku da abinci ba.
Kifi na kara fitowa
An samu labari mai kyau ga wasu jerin ababen da ke jerin bacewa. Wannan nau'in kifi ya bunkasa sosai a shekaru 10 da suka gabata, godiya ga matakin rage kamawa. Kashi 37 cikin 100 na kifin da ake tsoron za su bace saboda yawan kamawa.
Giwa kan hanya
Abu biyu da suke karkashin lissafin kasada su ne giwaye na dazukan Afirka da giwaye na Savannah. Dajin yana cikin kasadar bacewa haka ma Savannah na cikin hadari. Giwayen na tserewa masu farauta ta barauniyar hanya da mutanen da ke kara kutsawa cikin daji, inda dabbobi ke rayuwa, abin da ke kara janyo rikici tsakanin bangarorin.