Daga shugaba zuwa masoyan Bayern Munich
Uli Hoeness – Shugaban FC Bayern
"A kullum tunani na zai yiwu a sauya FC Bayern Munich daga karamin club izuwa fitacce a duniya." Wannan shi ne ya taimaka wa aikinsa a matsayin manaja. Sai dai a shekara ta 2014 an yanke masa hukuncin dauri a gidan yari na tsawon shekara uku da rabi, bisa kin biyan haraji. Amma zaman watanni 11 kacal ya yi. A lokacin Uli Hoeness ya ce ba shi ne karshensa a FC Bayern ba, kuma ya yi gaskiya.
Kamal Abu Lail (Nazareth, Isra'ila) – Masoyin Bayern
"Walau Bafalasdine ko Bayahude, idan Bayern suka zura kwallo su kan rungumi juna, a cewar Kamal. Ya kasance masoyin FC Bayern tun a shekarun 1970. "A lokacin ina dan shekaru 10 muna da akwatin talabijin mai kalar baki da fari. Muna yawan kallon wasanni kai tsaye: Rummenigge, Beckenbauer, Breitner, duk suna tashe a lokacin. Cikin sauri na shiga sha'awar 'yan wasan."
Philipp Lahm (Munich) –Wanda FC Bayern suka raina
Biyeyya, basira, nasara, Philipp Lahm shi ne misalin irin "basirar rainon Bayern". Dan shekaru 33 da haihuwa ya yi kusan shekaru 20 yana buga wa Bayern, yanzu ya yi ritaya. Ko da yake babu alamar matashin dan wasa gare shi. "Na fi kowa gajarta, watakila shi ne ya bani kwadayin bukatar samun nasara a shark pool wato FC Bayern."
Kanata Tokumoto (birnin Fuchu a Japan) – Masoyin Bayern
Kanata dalibin zamani na Club din FC Bayern Tsuneishi, a makarantar kwallon kafa da ke Fukushima. Dan shekaru 14 dan Japan yana da basira, shi ne ma ya sa FC Bayern suka tura mai horar da matasa na Club din izuwa can, domin su rika kula da shi. Mun ga basirarsa ne lokacin da Kanata ya buga wasa.
Samuel 'Sammy' Osei Kuffour (Accra, Ghana) – Tsohon dan wasa
Dan kasar Ghana ya iso Munich tun shekarunsa 17 a duniya, ya biyo ta Italiya. Uli Hoeneß ya kasance uba ga matashi Sammy, domin yana tare da shi a duk lokacin da ya shiga wata matsala a rayuwarsa. Musamman lokacin da 'yarsa ta rasu yayin da yake tashe a cikin dangin "Mia San Mia".
Camila Borborema (Rio de Janeiro, Brazil) –Masoyiyar Bayern
Wasu 'yan Brazil na cewa Camila na da tabin hankali. Domin duk da yawan Club-Club bila-adadin a kasarsu, amma 'yar shekaru 24 da haihuwa ta fi sha'awar Bayern. Akasarin irin burgewar da 'yan wasan Club din suka yi a wasan karshe na cin kofin duniya a 2002: "Oliver Kahn shi ne mafi burge ni a duniya, shi ne mafi abun ban mamaki a doron duniya. Ina kaunarsa fiye da komai."
Oliver Kahn (Munich) – Gwarzon gola
Ga wasu shi tamkar "Titan" ne, wasu kuma na daukarsa a matsayin tambarin "Bestia Negra," yayin da wasu ke daukarsa a matsayin mutum-mutumi irin Godzilla. Amma dai duk sun yarda da abu guda, wato babu wanda ya zama madadin FC Bayern kamar Oli Kahn. "Ina kiyaye dukkan martabobin Club din, domin nasara na samuwa ne kawai bisa kamala da dukkan abin da kake yi," a cewar tsohon golan.
Franz 'Bulle' Roth (Bad Wörishofen) – Gwarzon cikin gida
A shekara ta 1967 a wasan karshe na cin kofin Turai. Bayan karin lokaci ya zura kwallon da ya tabbatar da nasara a karawarsu da Glasgow Rangers. Ta haka ne kuma tarihin nasarar FC Bayern Munich ya samo asali. "Golan ya tinkaro ni kadan ya kada ni, amma sai ball din ya yi sama ya fada a raga. Na dauki kofin har kan gado na, a ranar nan na rungume shi har gari ya waye."
Giovane Élber (Mato Grosso, Brazil) – Tsohon dan wasa
Giovane Élber na da rayuwa kala biyu. A Brazil yana da shanu kimanin 5000 kusa da kan iyakar kasar da Boliviya. Amma a duk lokacin da Bayern suka nemeshi yana zuwa. Ya zagaya duniya a matsayin jakadan Club din. Ga dan kungiyar "Mia San Mia" yana duba baya a lokacin da yake bugawa Bayern, bisa nasa tsarin.
Rafael Noboa y Rivera (New York, Amirka) – Masoyin Bayern
Rafael an haifeshi a Puerto Ricokuma yana zama a New York, inda yake aiki a kamfanin sarrafa manhaja. Yana sha'awar FC Bayern tun shekaru 20 da suka gabata kuma bisa wani yanayi na daban. "Ina sha'awar wasansu, wasu lokutan tsarinsu ke burge ni. To amma wasu lokutan na kan zarce kima, don haka nake dan ja da baya. Bana son yin maitan kan abun da bana iya yi masa linzami."
Andy Brassell (London, England) – Dan jaridan wasanni
Andy na rubuta wa jaridar The Guardian kuma kwararre ne a "Talksport," wato mahawara kan wasanni, a daya daga cikin gidan rediyo mafi sanuwa a duniya. Ana martaba ra'ayoyinsa, kuma ya fi kwarewa kan Club na kasashen Jamus da Ingila. "Munich na da girma da kuma nasara, har ta kai ga wasu mutane a Ingila na cewa Bayern da Jamus duk abu guda ne."
Jaime Rodríguez Carrasco (Madrid, Spain) – Dan jaridan wasanni
Dan jaridan wasanni mai shekaru 38 a duniya daga EL MUNDO na sha'awar kwallon kafa a matsayin wani bangaren rayuwa kana a matsayin gasar wasanni. "A Madrid zan iya yanke hukunci ko birnin ya kwana shiru ko kuma kowa ya kwana cikin bacin rai." Babban labarinsa na shekara ba wai "El Clasico" amma sai idan Real Madrid suka kara da "La Bestia Negra" wato "Bakaken Dabbobi" ma'ana 'yan Club din Bayern.