Najeriya: Majalisa ta dage dokar zabe
December 22, 2021'Yan majalisar dattawan na Najeriya dai sun shiga da zumma da ma azamar tattaunawa a kan wannan batu da ya tayar da kura da hayaniya a tsakanin 'yan majalisar, tun bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu a kan gayaran fuska da aka yi wa dokar zaben. Sanatocin dai sun shiga zaman sirri na tsawon sa a guda, kafin daukar matakin. Wannan batu na kin sanya hannu a kan gyare-gyaren da aka yi ga dokar zaben dai, ya harzuka 'yan majalisar da dama.
Sanatoci sama da 80 suka sanya hannu na amincewa su yi wa lamarin tukin tsaye na amfani da karfin ikonsu a kan shugaban Najeriyar. Tuni dai ra'ayoyin 'yan Najeriya suka rarraba a kan wannan batu, inda kungiyoyin farar hula ke son majalisar ta dauki matakin da ya dace. A karshe dai majalisar dattawan ta amince da kasafin kudin 2022, inda ta bi sawun ta wakilai. Duka majalisun biyu dai sun tafi hutun karshen shekara sai zuwa watan Janairun badi, domin ci gaba da aikinsu na kafa dokoki da sa ido a kan bangaren zartaswa a kokarin tsawatarwa juna.