1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Siriya sun kashe shugaban IS

December 2, 2022

Rundunar soji a Siriya ta dauki alhakin kashe shugaban kungiyar mayakan IS a wani farmaki da ta kai kudancin kasar a watan Oktoban da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4KOnI
Jami'in sojin Kurdawa na Syrian Democratic Force (SDF)
Hoto: Baderkhan Ahmad/AP/picture alliance

An kashe Abu al-Hassan al-Hashemi al-Quraishi ne a wani farmakin da dakarun rundunar suka kai garin Deraa da ke kudancin lardin da ke fuskantar hare-haren 'yan tawaye.

Wannan dai shi ne karon farko da aka kashe wani jagora na kungiyar IS a kudancin kasar maimakon arewacin kasar da ake karkashin ikon bangarori daban-daban, ciki har da wandada ke samun goyon bayan Amirka. Sai dai kuma Dakarun Kurdawa na Syrian Democratic Force (SDF) da ke samun goyon bayan Amirka sun ce, ba su da hannu a farmakin na watan October, kamar yadda ita ma ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta bayyana.

A shekarar 2018 dai yankin na Deraa ya koma karkashin ikon dakarun kasar biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma wanda Rasha ta jagoranta, inda aka ga yadda 'yan tawaye suka mika makamansu a wancan lokacin.