1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da tallafi wa 'yan tawayen Siriya

December 12, 2013

Amurka da Britaniya sun sanar da dakatar da ba wa 'yan tawayen Siriya da ke fada da gwamnatin Bashar al-Assad tallafi na wasu kayayyaki da suka kunshi magunguna da motoci

https://p.dw.com/p/1AXgw
Hoto: Reuters

Amurka da Britaniya sun dakatar da tallafin magunguna da motoci wa 'yan tawayen da ke yankin arewacin Siriya. A cewar Washington hakan na zama martani ne ga rahotannin kwace wasu sansanoni daga wajen sojin adawa da gwamnatin Siriya da 'yan tawayen suka yi kan iyakar kasar da Turkiyya. Tun bayan barkewar rikicin Siriyar a watan maris din shekara ta 2011 ne dai, gwamnatocin Amurka da na Britaniya suka ki bayar da agajin makamai wa kungiyoyin 'yan tawayen, domin gudun fadawarsu hannun kungiyoyin tarzoma da ke da alaka da Al-qaeda. Matakin dakatar da kai daukin na yanzun, nada nasaba da gudun kada kayayyakin tallafin su fada hannun da basu da ce ba. Sai dai Amurka ta ce, matakin ba zai shafi bayar da agaji ga mabukatun Siriyar ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu