1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da tattara kudin yaki da Corona a Kamaru

Gazali Abdou Tasawa
April 30, 2020

Gwamnatin kasar Kamaru ta ba da umurnin dakatar da shirin tattara kudade daga jama'a wanda madugun 'yan adawar kasar Maurice Kamto ya kaddamar da nufin yaki da annobar Coronavirus a kasar.

https://p.dw.com/p/3baYa
Frankreich Paris |  kamerunischer Oppositioneller Maurice Kamto
Hoto: DW/E. Topona

Gwamnatin ta bayyana shirin da kasancewa haramtacce tare kuma da bai wa kamfanonin salula guda biyu na Orange Cameroun da na MTN Cameroun wadanda ke aikin tattarar kudin da su rufe asusun ajiyar kudin wanda aka bude a karkashin shirin domin ajiyar kudaden taimakon.

 A watan Aprilun da ya gabata ne dai madugun 'yan adawar kasar ta Kamaru ya kaddamar da wannan shiri nasa na neman tallafi kudi a ciki da wajen kasar ta Kamaru domin gudanar da ayyukan yaki da annobar Coronavirus a kasar inda kawo yanzu cutar ta harbi mutun dubu daya da 830 ta kuma halaka 61 daga cikinsu.