1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan an koma makaranta

Abdoulaye Mamane Amadou
September 18, 2021

A Afghanistan daliban makarantun sakandare da na gaba da sakandare sun koma karatu a wannan Asabar. Sai dai komawar ta shafi ne kawai maza ba tare da mata ba.

https://p.dw.com/p/40VkF
Afghanistan | Trennung von weiblichen und männlichen Studenten an der Universität Kabul
Hoto: Social media handout via REUTERS

Ministan harkokin ilimin Afghanistan ya bayyan cewa daukacin daliban makarantun bokon gaba da sakandare da malumansu maza, za su koma makaranta. Kwanaki 10 bayan da takwarorinsu na jami'o'in kasar masu zaman kansu suka koma, sai dai wannan matakin ya sha suka daga hukumar kula da yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya Unicef.

Wannan lamarin na zuwa a daidai lokacin da ko wannan Asabar, wasu hare-haren nakiyoyi uku sun kashe akalla mutum biyu a birnin Jalalabad. Shaidu sun ce daya daga cikin hare-haren kuma an kai shi a kan wata motar da ke dauke da mayakan Taliban.

Batun Afghanistan na kan gaba daga cikin jerin batutuwan da za su dauki hankali a yayin babban taron koli na Majalisar Dinkin Duniya na makon gobe.