Taron rage dumamar duniya
October 31, 2021Shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 26 da aka yiwa lakabi da COP26, Alok Sharma ya baiyana taron Glasgow kan sauyin yanayin da cewa ita ce dama ta karshe ta rage dumamar duniya da maki daya da rabi a ma'aunin Celcius.
Da yake bude taron a yau Lahadi Alok Sharma ya yi tsokaci kan mummunan tasirin da gurbataccen hayakin masana'antu ya yi ga dumamar duniya tsawon shekaru 150 da suka gabata.
Kwararrun masana muhalli sun yi gargadin cewa daukar managarcin mataki cikin shekaru goma masu zuwa shi ne kadai zai sauya tasirin illar da ake fuskanta daga dumamar yanayi a halin yanzu.
A nasa bangaren Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bukaci shugabannin duniya dake halartar taron su nuna kwakkwaran kudiri na shawo kan dumamar duniyar idan ana so a cigaba.