Dan adawan Gambiya ya rasu a hannu gwamnati
April 16, 2016Rahotanni daga Banjul babban birnin kasar Gambiya na cewa, wani babban dan adawan kasar mai suna Solo Sandeng ya rasu yayin da yake tsare a hannun jami'an tsaron kasar a cewar jam'iyyarsa ta UDP da kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International.
A ranar Alhamis ce dai da ta gabata, 'yan sandan kwantar da tarzoma suka kama dan adawan na kasar ta Gambiya, bayan da ya jagoranci wata zanga-zangar nuna kin jinin shugaban kasar Yahya Jammeh.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin mutuwar dan adawa ba a cewar wakilin kungiyar ta Amnesty International, wanda ya yi kira ga hukumomin kasar da su gaggauta gudanar da bincike, tare da sakin dukannin mutanen da ake tsare da su 'yan jam'iyyar adawa ta UDP.
A baya dai shugaban jam'iyyar Ousainou Darboe, ya ce wasu mata biyu da aka kama cikin masu zanga-zangar na cikin doguwar suma a halin yanzu.