1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan Nijar ya lashe gasar gwanin kwallon na DW

Usman Shehu Usman
February 1, 2017

Mun dai samu wanda ya yi nasara! Dan wasan gaba na Dortmund Aubameyang ya lashe zaben DW na gwarzayen Bundesliga a shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/2Wo19
Fußball Bundesliga 1. Spieltag Borussia Dortmund - Borussia Mönchengladbach
Hoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

Mun samu wanda ya yi nasari! Dan wasan gaba na Dortmund ya lashe zaben DW na gwarzayen Bundesligaa shekara ta 2016. Masu amfani da shafin DW- sun yanke shawara cewa,Pierre-Emerick Aubameyang na Borussia Dortmund shi ne gwarzonsu a a tsakanin 'yan wasan 2016 na Bundesliga. Wannan kuwa yana da mahimmamnci.Gwanin kai harin, tun farkon bana ya tafi Afirka don yi wa kasar ta haifuwa Gabon wasa a kasar cin kofin kwallon kafan Afirka wanda ake bugawa a Gabon din. Ya dai zura wa kungiyar Dortmund kwallaye har 23 a wasannin Bundesliga na bara. Yawan wadannan kwallaye da ya ci da kuma kasancewarsa mutum mai bla’in gudu, hakan ya sa ya zama zakara a kulub din na Borussia Dortmund. Bugu da karin kyaukyawan halayensa  sun kara wa Aubameyang kima. Irin riguna wasa da kuma askin da ya ke yi daban suke da na sauran yan wasa .

Mutane da suka zo na daya danan biyu da uku da kuma sakamakon zaben

Pierre-Emerick Aubameyang      kashi  34,4 cikin dari

Robert Lewandowski                     kashi 32,8 cikin dari

Joshua Kimmich                            kashi 8,5 cikin dar

A yayin da "Auba" ke muranar lashe zaben DW, Akwai mutane hudu da suka yi nasara daga cikin wadanda suka shiga gasar zaben. Wanda yazo na daya da za’a bai wa rigar Bundesliga- bayan zaben shi ne Mahamane Mounkaila Mato daga Jamhuriyar Nijar. Sai na biyu da za su samu kyautar DW-da ba ambata ba , sune Adriana Suárez daga Kwalambiya, Alma Rosa Ruiz dan Mexiko da Leonidas Bakoylas dan kasar Girka.

Za’a sanar wa wadanda suka lashe gasar a rubuce cikin kwanaki da ke tafe. Muna taya murna da kuma mika matukar godiya ga wadanda suka shiga gasar.