March 19, 2020
Talla
A tsakanin matasa sakamakon tsoron kamuwa da wannan cuta ta numfashi da farko sun fara daukar wanna al'amari a matsayin wasa, kafin ta rikide ta zama babbar magana bayan da masu jinin a jika suka shiga sahun masu rasa rayukansu sakamakon kamuwa da corovirus. Ko da 'yan Afirka da walau suke karatu a kasashen Turai ko kuma suka fara aiki sun gano girmar matsalar, lamarin da ya sa suka soke duk abubuwan da suka tsara kama daga bukukuwa zuwa karatu da motsa jiki.