Ginin cibiyar adana makamai a Saudiya
February 20, 2019Talla
A baya dai jami'an fadar mulki ta White House wadanda suka hada da tsohon mai ba da shawara a harkar tsaro Micheal Flyn sun jagoranci batun makaman, duk kuwa da cewar jami'an tabbatar da ka'idojin mulki sun soki shirin. Tun da fari cikin wani rahoto da zauren majalisar dokokin ya fitar mai shafi 24, bakin 'yan majalisar kasar ya zo daya game da fargabar Saudiyya za ta samu damar amfani da kimiyyar Amirka wajen kirkirar makaman nukiliya. Tsohon mai ba da shawara a harkar tsaron Micheal Flyn dai, na jiran hukunci bayan samun sa da karya a binciken kutsen da kasar Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amirka na shekara ta 2016.