1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Daruruwan marasa lafiya da dubban mutane suka fake a asibiti

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 13, 2023

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce jarirai da ke cikin kwalba sun mutu sakamakon katsewar wutar lantarkin, yana mai nuna takaicinsa a kan hakan.

https://p.dw.com/p/4YjON
Hoto: Saeed Jaras/APA/IMAGO

Daruruwan marasa lafiya da kuma dubban mutanen da ke neman mafaka a babban asibitin Zirin Gaza wato Al-Shifa ke cikin halin dimuwa da tashin hankali, sakamakon fafatawar da sojojin Isra'ila da mayakan Hamas ke yi yanzu haka a bakin harabarsa.

Karin bayani:Hukumomi a Gaza sun ce wasu hare-haren Isra'ila sun fada kan asibitoci guda uku a juma'ar nan

Wani shaidar gani da ido ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa gwabzawar ta kazanta ne tun a jiya Lahadi zuwa wayewar garin yau Litinin, a daura da asibitin da hukumar lafiya ta duniya WHO da ma sauran hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar da cewa yana dauke da marasa lafiya sama da dubu uku, cikin yanayin rashin wutar lantarki da ruwan sha da abinci da kuma man fetur.

Karin bayani:Red Cross ta damu da kashe-kashen kananan yara a Gaza

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya tabbatar da cewa jarirai da ke cikin kwalba sun mutu sakamakon katsewar wutar lantarkin, yana mai nuna takaicinsa a kan hakan.