Mali ta kara sulhu da 'yan tawaye
August 6, 2022Gwamnatin rikon kwarya ta mulkin soja a Mali ta cimma matsaya ta shimfida zaman lafiya da mayakan 'yan tawayen Abzinawa da ke arewacin kasar, inda za ta ba wa mutane dubu 26 daga cikin mayakan a guraben aiki.
Fadar mulki ta birnin Bamako ta ce za a dauki mutun dubu 13 a zangon farko na aiwatar da yarjejeniyar, kana bayan ba su horon sanin makamar aikin soja za su koma a yankunan arewacin kasar don kara tabbatar tsaro daga nan zuwa shekarar 2024.
A shekarar 2015 ce dai gwamnatin Mali ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya a binrin Alger da 'yan awaren na Abzinawa masu ikrarin kafa kasar Azawak a arewacin Mali, sai dai an fuskanci tarnaki a gabanin fara aiki da yarjejeniyar bayan da aka kifar da gwamnatin farar hula a kasar watanni da dama da suka gabata.