Dlamini-Zuma mace ta farko a babban muƙamin AU
July 20, 2012A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali kan zaɓen Nkosazana Dlamini-Zuma 'yar ƙasar Afirka ta Kudu a muƙamin shugabar hukumar ƙungiyar tarayyar Afirka AU.
A rahoton da ta buga, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce "Dlamini-Zuma ƙwararriyar 'yar siyasa nahiyar Afirka ce dake da ƙarfin faɗa a ji. Matar mai shekaru 63 daga ƙabilar Zulu ta bambamta da magabacinta Jean Ping wanda ya fi mayar da hankali akan cika aikin takarda maimakon ganin a ƙasa. Dlamini-Zuma mai son samun sakamakon ayyukan da ta sa a gaba ne, saboda haka bisa ga dukkan alamu Afirka ta yi kyakkyawan zaɓi."
Ita ma a labarinta mai taken ƙwararriyar 'yar siyasa a kan babban muƙamin tarayyar Afirka, jaridar Neues Deutschland ta fara ne da cewa:
"Da wannan zaɓen na 'yar Afirka ta Kudu Dlamini-Zuma a matsayin shugabar hukumar ƙungiyar AU, a karon farko an samu mace a muƙami mafi girma a cikin ƙungiyar ta AU. Tun daga shekarar 1976 Dlamini-Zuma wadda likita ce ta fara sana'arta a zaman ƙaura da ta yi a Birtaniya. 'Yan gwagwarmayar neman 'yancin ƙungiyar ANC suna tunawa da ita a zama ɗaya daga cikin 'yan fafatukar ANC a birnin London. Sai dai ba ta ɗauki hankalin duniya ba sai daga shekarar 1994 inda a sabuwar ƙasar Afirka ta Kudu ta zama minista. Kuma a matsayinta na ministan harkokin wajen Afirka Ta Kudu tun a lokacin shugabancin Thabo Mbeki, ta samu ƙwarewa a fannin aikin diplomasiya na ƙasa da ƙasa."
Ita kuwa jaridar die Tageszeitung ta leƙa birnin Legas ne cibiyar hada-hadar kasuwanci a tarayyar Najeriya tana mai cewa hari akan tsibirin Venedig na Afirka tana mai nuni da tayar da mazauna unguwar Makoko dake kan ruwa a birnin na Legas.
"A tsakiyar birnin Legas mutane kimanin dubu 100 ke zaune a wata unguwar marasa galihu dake kan ruwa a cikin bukkukokin katako dake ƙarƙashin wata babbar gada, amma yanzu mahukuntan Legas sun fara rushe waɗannan matsugunai. Wa'adin sa'o'i 72 da hukumomin suka ba wa mazauna unguwar da su tattara na su ya nasu su bar wurin sun yi kaɗan. Dalilin tayar da unguwar shi ne gidajen na ƙarƙashin manyan wayoyin wutar lantarki masu hatsari. Amma tambaya a nan ita ce ko rusau ɗin za ta samar da wani ƙarin tsaron ko kuma dai manufa ita ce unguwar ta Maroko ba ta dace da fasalin birnin Legas ɗin a yanzu ba koma ake son a kawar da ita?
UNESCO ta yi ƙasa inji jaridar Neue Zürcher Zeitung, sannan sai ta ci-gaba kamar haka: "A karon farko a ranar Talata ƙungiyar kyautata ilimi, kimiyya da al'adu ta Majaliar Ɗinkin Duniya ta yi bikin ba da lambobin yabo da ƙasar Equitorial Gini ta ɗauki nauyinsa. Bikin da aka kashe dala miliyan uku ya sha suka kasancewa kyautar ta fito ne daga shugaban mulkin kama karya Obiang Nguema wanda manufarsa ita ce wanke kansa."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala