Matakan kariya na masu ababen hawa a birnin Yamai
October 2, 2018Galibin motocin da ke wucewa na 'yan kasuwa da masu zaman kansu na sanye da "belt wato ceinture de securite" a matsayin matakan kariya kamar yanda dokar ke cewa inda galibin su kuma masu Babura ke wucewa da hular kwano lamarin da ke tabbatar da cewar dokar ta fara aiki gadan-gadan ke nan.
Dokar dai da ke zaman zakaran gwajin dafi ga sauran wasu yankunan kasar ta tanadi matakin hukumta duk wanda aka kama da laifin tare da tara daga jika 10 zuwa 50 na kudin Sefa ga masu motoci ko kuwa jika 5 zuwa 10 ga duk masu baburan da aka kama ba hular kwano sai dai ga alama matuka motocin safa sun ce za su kalubalanci wannan doka.
Hukumomin birnin Yamai na cewar dokar ta shafe akalla watanni 16 kafin soma aiki da ita duk da yake masu ababen hawa sun soma nuna mata kasawa. Akalla mutun fiye da 900 ne suka hallaka a shekarar bara kawai sakamakon yawaice yawaicen hadurran ababen hawa kamar yanda alkalumman hukumomin suka tabbatar lamarin da kuma ayanzu hukumomin suka ce za su kai ga magancewa