1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump ne dan takarar jam'iyyar Republican

Abdourahamane HassaneJuly 22, 2016

Hamshakin mai kudin nan na Amirka Donald Trump ya amince da nadin da jam'iyyarsa ta Republican ta yi masa na tsayawa takara a zaben shugaban kasar na shekarar 2016

https://p.dw.com/p/1JU3S
USA Republican National Convention in Cleveland Donald Trump Rede
Hoto: Reuters/M. Segar

Da yake yin jawabi a gaban wakilan jam'iyyar kusan dubu biyu da kuma wasu miliyoyin Amirkawan a Cleveland da ke cikin Jihar Ohio,Trump ya ce aiki na farko da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai idna ya zama shugaban kasa, shi ne na kuubtar da al'ummar Amirka daga halin rashin tsaro na kisan ba gayra na jama'a da kuma ta'addanci da ke zama babbar barazana ga rayuwar jama'a.