1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump shi ne zai wa jam'iyyar Republican takara

Yusuf BalaJuly 20, 2016

Sunan Trump na zuwa a lokacin da 'yan Republican suka yi wa Clinton rubdugu na suka a yayin da ake tunkarar zaben shugaban kasa a Amirka.

https://p.dw.com/p/1JSNT
USA Donald Trumps Rede über seine Nominierung
Donald Trump dan takarar Amirka da ya ja hankalin duniya a lokacin kamfeHoto: Reuters/M. Segar

Dantakarar shugabancin Amirka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ta tabbata a hukumnace shi zai fafata da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton a zaben shugaban kasa da Amirka za ta yi a watan Nuwamba mai zuwa. Wannan dai na zuwa ne bayan da a ranar Talata a babban taron jam'iyyar ta Republican a birnin Cleveland na jihar Ohio aka bayyana dan takarar.

Bayyana Trump da ke zuwa a rana ta biyu na babban taron jam'iyyarsa ta Republican da aka yi wa lakabi da taken "Maida Amirka bisa turbar aiki" maimakon bayyana hanyoyi da jam'iyyar za ta yi aiki, masu bayanai a taron sun maida hankali wajen suka ga 'yar takarar jam'iyyar Democrats Hillary Clinton.

A lokacin da yake jawabi a Ostareliya Joe Biden mataimakin shugaban Amirka bayan da aka tambaye shi kan inda kasar ta Amirka ta nufa ga su Trump a gaba a zabe, ya ce dangantakar kasar Amirka ta harkokin kasuwanci da sauransu na nan daram a hannun Amirkawa masu manufa.