1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Donald Trump ya ayyana lashe zaben Amurka

November 6, 2024

Donald Trump na jam'iyyar Republican ya lashe zabe a North Carolina da Georgia da kuma Pennsylvania, jihohin da ke kasancewa zakaran gwajin dafi ko kuma raba gardama da ke da matukar tasiri a siyasar Amurka.

https://p.dw.com/p/4mgVt
Donald Trump da iyalinsa
Donald Trump da iyalinsaHoto: Carlos Barria/REUTERS

Republican ta kuma samu gagarumar rinjaye a kujerun majalisar wakilai da ta dattawa a jihohin West Virginia da Ohio. A can kuwa jihohin New York da California Jam'iyyar Democrats ta Kamala Harris na ci gaba da mamaya duk da cewa a tarihin jihohin Republican ce ke lashe kujerun 'yan majalisa.

Karin bayani: Harris na zawarcin kuri'un musulmi a Michigan

A wani labari kuma da ke daukar hankali a siyasar kasar, 'yar takarar majalisar wakilan Amurka musulma dake da tsatso da Larabawan Falasdinu ta Jam'iyyar Democrats Rashida Tlaib, ta lashe zabe a jihar Michigan.

Karin bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka 

Rashida Tlaib na gaba-gaba wajen sukar manufofin gwamnatin Amurka kan gudummuwar makamai da take bai wa kasar Isra'ila. A shekarar da ta gabata 'yar majalisar ta fuskanci matsin lamba da kuma bincike daga hukumomin Amurka kan furucin da ta yi bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba.

Rashida ta lashe zaben fidda gwani a mazabarta ba tare da hamayya ba kuma ta kada 'dan takarar jam'iyyar Republican James Hooper da ke zawarcin kujerar majalisar wakilan yankin.