Donald Trump ya gana da Benjamin Netanyahu
February 15, 2017Talla
Shugaban Amirka Donald Trump ya ce MDD ta yi wa Isra'ila rashin gaskiyya sakamakon goyon bayan da take bayerwa na ganin an girka kasashe biyu watau Isra'ila da Falasdinu.Trump ya bayyana haka ne a lokacin wani taron manema labarai hadin gwiwa da ya yi tare da firaminsta na Isra'ila Benjamen Netanyahu wanda ke yin ziyara a Amirka.