1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu: Shekaru biyu na sulhu

February 24, 2022

A wannan makon, gwamnatin hadaka ta Sudan ta Kudu ta cika shekaru biyu da kafuwa. An dai dorawa gwamnatin nauyin dawo da zaman lafiya bayan farfado da yarjejeniyar sulhu da aka rattabawa hannu a 2018.

https://p.dw.com/p/47XdR
Sudan ta Kudu I Salva Kiir I Riek Machar | Gwamnatin Hadaka
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da tsohon mataimakinsa mai adawa Riek MacharHoto: AFP/M. Kuany

An dai cimma yarjejeniyar sulhun ta Sudan ta Kudun da aka rattabawa hannu a 2018 ne, a tsakanin Shugaba Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa kana madugun adawar kasar Riek Machar. Muhimman kudirori a yarjejeniyar wadanda suka danganci sabunta gine-gine da yiwa tattalin arzikin kasar garanbawul da inganta fannin shari'a da tabbatar da adalci, har yanzu gwamnatin ba ta aiwatar da su ba. Kasashen duniya masu bayar da tallafi ba su ji dadin rashin ci-gaban da aka samu ba. Christian Bader Jakadan kungiyar Tarayyar Turai a Sudan ta Kudu, ya yi tsokaci kan dalilin hakan. "Ba wai saboda yarjejeniyar ba ta da kyau ba ne, sai dai saboda babu kwakkwaran kudiri na aiwatarwa. Idan da akwai kudirin a zuci, ba sai an bukaci wata yarjejeniya ba abubuwa za su gudana ne kawai salin-alin." 

Sakataren gwamnatin Sudan ta Kudun Martin Elia Lomuro ya ce raunin tattalin arziki ya sa ana fuskantar babban kalubale wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar. A cewarsa su ma kasashen duniya suna da laifi na rashin mutunta dokar haramcin sayar da makamai da aka sanya kusan shekaru 10 da suka wuce, wanda ya kawo tarnaki wajen aiwatar da yarjejeniyar. A shekarar 2012 kasar Sudan da kuma sabuwar kasar Sudan ta Kudu wadda ta samu 'yancin kai, sun yi arangama a kan iyakar da Sudan ke kira Heglig ko kuma Panthou da yaren Juba. An yi ta gwagwarmaya kan mallakar rijiyoyin mai. A 2013 kuwa aka ga barkewar yakin basasa, wanda aka kawo karshensa ta hanyar yarjejeniyar da aka cimma a 2018. Wa'adin gwamnatin hadakar dai zai kawo karshe ne a watan Fabarairun 2023, inda ake fatan gudanar da zaben gama gari ba tare da wani shamaki ba.