1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Yemen

December 27, 2024

Kimanin mutane 10,000 ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Sanaa na Yemen bayan da Isra'ila ta kai hari kasar.

https://p.dw.com/p/4odTK
Hoto: Yahya Arhab/epa/dpa/picture alliance

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Sanaa na Yemen, kwana guda bayan da jiragen Isra'ila suka kai farmaki kan sansanonin 'yan tawayen Huthi, a matsayin martani ga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka da 'yan tawayen suka kai mata. Masu boren sun yi ta tada jijiyoyin wuya tare da daga kwalaye yayin da suke sauraron jawaban nuna adawa da Isra'ila.

Karin bayani: Isra'ila ta kai jerin farmaki a Yamen

A kalla mutane shida ne suka mutu a harin da Isra'ila ta kai filin jirgin saman Sanaa, inda shugaban Hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ke jiran lokacin tashin jirginsa. Jirage sun ci gaba da tashi da sauka a filin jirgin, duk da lalacewar wasu sassan filin. Shi ma dai, shugaban WHO ya bayyana cewa ya sauka lafiya da tawagarsa a Jordan, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya.