Duniya na dumama fiye da yadda ake tsammani
September 23, 2019Talla
A wani rahoto da ta fitar hukumar kula da yana yi ta duniya ta nuna cewa a 'yan shekaru da suka wuce yanayin zafi ya karu yayin da koguna da koramus uka cika makil sannan gurbatar hayakin masana'antu ya karu matuka.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci rage hayakin Carbon nan da shekara ta 2050 domin tsaftace muhalli daga gurbatacciyar iskar.
A waje guda kuma kasashen Afirka za su gabatar da kiran ayyana dokar ta baci kan muhallin domin taimaka musu kare illomin gurbatar muhalli a nahiyar.