1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wutar daji na barazana ga duniya

Ramatu Garba Baba ZMA
February 23, 2022

Akwai fargabar duniya za ta fuskanci matsanancin yanayi a shekaru masu zuwa a sakamakon matsalolin da dumamar yanayi ke haifarwa in ji Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/47RxZ
Australien Waldbrände Feuer Buschfeuer
Hoto: Paul Kane/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar, za a fuskanci karin matsanancin wutar daji a shekaru masu gabatowa saboda dumamar yanayi, kuma gwamnatoci ba za su kasance cikin shirin fuskantar irin mace-mace da asarar da wutar za ta janyo ba.

Rahotan da Hukumar Kula da Muhalli ta majalisar ta fitar, na nuni da cewar, ko kokarin da ake yi na fitar da hayaki marasa guba ba zai yi wani tasiri dakatar da wannan matsanancin yanayi da ke tafe ba. Ya zuwa karshen wannan karnin a cewar hukumar, duniya za ta fuskanci yanayi na wutar daji makamancin wadda kasar Australiya ta fuskanta a shekarun 2019-2020 da aka yi wa lakabi da suna "Black summer".