1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta taru kan muhalli wasu ba wurin kwana

October 18, 2016

Taron da ake wa lakabi da Habitat na uku (III) na zuwa yayin da aka yi kiyasin cewa kafin shekara ta 2050 kowane mutum daya daga cikin mutane uku zai kasance mazaunin birni ne.

https://p.dw.com/p/2RObC
Nigeria schwimmender Slum in Lagos
Hoto: picture-alliance/AA/ABACAPRES.COM/M. Elshamy

Daga ranar 17 zuwa 20 ga watan nan na Okotoba ake gudanar da babban taron duniya kan muhalli da tsarin ci-gaban birane mai dorewa. Taron da ake wa lakabi da Habitat na uku (III) na zuwa yayin da aka yi kiyasin cewa kafin shekara ta 2050 kowane mutum daya daga cikin mutane uku zai kasance mazaunin birni ne. Samar da wannan tsari da zai dore zai dogara ne kan irin kudurorin da taron wanda MDD ta shirya, zai zartas.

Birane na zama wurin da ake fatan samun kyakkyawar rayuwa da ilimi da aikin yi da kuma wata kyakkawar makoma. A duniya baki daya birane na zama wasu cibiyoyin hada-hadar tattalin arziki da ke samar da kashi 70 cikin 100 na jimillar kayayyakin cikin gida na kasa. Ko da yake kaso kadan suke da shi na fadin kasa, amma suna cin makamashi da yawan gaske. Wani nazarin Majalisar Dinkin Duniya ya ce birane na amfani da fiye da kashin 60 cikin 100 na makashin da duniya ke samarwa, su ne kuma ke da alhakin fidda kashi 70 cikin 100 na hayaki mai gurbata yanayi da shara kashi 70 cikin 100 a duniya.

Brasilien Rio de Janeiro Luftaufnahme
Manyan birane na fama da cinkoso da bata muhalliHoto: Getty Images/M.Tama

Sai dai Eva Dick ta cibiyar nazarin manufofin ci gaban kasa ta Jamus ta ce birane na taka muhimmiyar rawa wajen cimma muradun ci-gaba.

"In ba tare da birane ba, zai yi wahala a iya cimma muradun ci-gaba. Saboda haka tun yanzu da yawa ke wa taron Habitat na uku kallon wani babban taron farko na aiwatar da muradun ci-gaban al'umma."

Ko shakka babu biranen na da manyan kalubale a gabansu a dole suke daukar wasu nauye-nauye, sai dai babban taron na MDD da ake shiryawa ko wasu shekaru 20 ke da fada a ji. Amma kudurin "Sabuwar Ajandar Alkarya" wato "New Urban Agenda" da taron na bana tsakanin 17 zuwa 20 ga watan nan na Oktoba a garin Quito na kasar Ekwado zai zartas ba zai zama dole dukkan kasashe su yi aiki da shi, ya na a matsayin shawara da nufin samun ci-gaba mai dorewa a birane.

Pakistan Handlesen auf der Straße
Da dama a birane na kwana a gefen hanya saboda rashin wurin kwanaHoto: Imago/Pak/IMAGES/Ilyas Dean

Monika Zimmermann ita ce mataimakiyar darakta janar na wata kungiyar kasa da kasa da ta kunshi birane da kananan hukumomi da hukumomin yankuna fiye da 1500 ta ce samar da kundin tafiyar da aikin ci-gaban biranen shi ne kashin bayan manufar da aka sa a gaba.

Sake fasalin birane aiki ne na duniya baki daya. Nan da shekaru 35 masu zuwa dole ne a samar da karin gidajen kwana ga miliyoyi dubbai na mutane. Dole ne kuwa a hada da samar musu da yanayin zaman lafiya da lumana da kwanciyar hakali tare da kyautata zamantakewarsu.