1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW na kara karfafa hulda da kafofin Afirka

Abdourahamane HassaneJune 14, 2016

A karon farko DW ta cimma wata yarjejeniya da gidajen talbijan da rediyio na kasashen Afirka da dama a kan batun kare muhali.

https://p.dw.com/p/1J6ci
Bonn Global Media Forum GMF 01 | Opening Ceremony Peter Limbourg
Hoto: DW/M. Müller

Wakilai na gidajen rediyon da TV na Kenya da Najeriya sun rataba hannu a nan Bonn tare da shugabannin DW kan wata yarjeniya ta yada wani shirin kare muhali watau Eco Afirca na DW.

Shirin dai na Eco Afirca ya kan duba muhimman misalai na irin sauyin da a kan samu a kasashen Afirka da ma Turai a game da fafutukar kare muhali.Da yake yin jawabin bayan saka hannu a kan yarjejeniya shugaban tashar DW Peter Limbourg ya ce shirin wata dama ce ta ambato matsalolin kare muhali tare da kafofin abokanan hulda.Misali Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da lamarin canji yanayi ke yin tasiri a rayuwar al'umma ta yau da gobe.