1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta 'yancin fadin albarkacin baki

Kaschel Helena
February 19, 2019

Anabel Hernandez 'yar jarida ce wadda ta yi fice wajen bada rahotanni kan masu fasakwaurin miyagun kwayoyi da kuma tabargazar cin hanci da rashawa a kasar Mexico

https://p.dw.com/p/3DgYa
Interview mit der Gewinnerin des DW Freedom of Speech Award 2019: Anabel Hernández
Hoto: DW/V. Tellmann

Tsawon shekaru 20 Anabel tana aiki ba tare da jin tsoro ko fargaba ba, inda ta ke bankado ayyukan masu fasakwaurin miyagun kwayoyi da tabargazar cin hanci da rashawa a rahotannin da ta ke bayarwa.

Bisa la'akari da kwazon ta da kuma jajircewa tashar DW ta karrama ta da lambar yabo ta bana ta yancin fadin albarkacin baki.

Shugaban tashar DW Peter Limbourg ya yabawa kwazon yar jaridar Anabel Hernandez mai shekaru 47 da haihuwa yana mai cewa labaran da ta ke bayarwa suna cike da bincike da kuma tsantsan gaskiya kuma misali ne abin koyi ga dukkan yan jaridu. Ita ma da take tsokaci Anabel Hernandez ta yi jawabi tana mai cewar:

"Wannan karramawa ta zo a wani lokaci mai matukar muhimmanci a rayuwa ta, saboda bayan Mexico na kan ji tamkar bani da kowa ina cikin kadaici, a wasu lokutan na kan ji kamar aikin da nake yi bai kai yadda zan iya sauya abubuwan da nake so na sauya ba. To amma wannan karmawa a wajen ta bi gaban karramawa kawai, kwarin giwa ce da kuma goyon baya ba gare ni kadai ba amma ga yancin fadin albakacin baki da kuma yancin al'ummar kasar Mexico. Kuma ina ganin irin wannan karramawa daga wata kafar yada labarai ta duniya za ta taimaka mana cigaba da ayyukan mu."

Karo na biyar kenan a jere tashar Deutsche Welle na bayar da lambar yabo don karrama mutanen da suka yi fice wajen kare hakkin dan Adam da kuma yancin fadin albarkacin baki.

Za a mika lambar yabon ga Anabel tare da karrama ta a babban taron yan jaridu da kafofin yada labarai da aka yiwa lakabi da Global Media Forum wanda tashar DW ke daukar nauyinsa a duk shekara.

An haifi Anabel Hernandez a kasar Mexico, ta kuma fara aikin jarida a shekarar 1993 da wata jarida Reforma yayin da take matsayin daliba a jami'a.

A shekarun da suka wuce Hernandez ta yi fice a Mexico a matsayin 'yar jarida mai binciken kwakwaf inda ta wallafa labarai da suka bankado badakalar cin hanci da rashawa a gwamnati da cin zarafi ta hanyar lalata da kuma safarar miyagun kwayoyi.