1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola: An takaita zirga-zirga a Saliyo

Ahmed SalisuDecember 25, 2014

Al'ummar Port Loko da ke arewacin Saliyo sun wuni cikin gidajensu bayan da gwamnati ta sanya doka ta hana zirga-zirga a yankin domin dakile bazuwa cutar nan ta Ebola.

https://p.dw.com/p/1EA8w
Symbolbild - Ebola Virus
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun da sanyin safiyar yau ne dai ministan yada labarai na kasar Alpha Kanu ya sanar da wannan aniya ta gwamnatin kasar inda ya ce babu shiga babu fita a yankin gaba daya.

To sai dai ya ce gwamnati za ta rika rarraba abinci da kayan masarufi ga al'ummar yankin domin kada su shiga yanayi na kunci domin kuwa ba za a dage wannan haramci na zirga-zirga da aka sanya ba inji gwamnati har sai an samu raguwar bazuwar cutar Ebola.

Saliyo dai na daga cikin kasashen Afirka ta yamma ukun nan da cutar ta Ebola ta yi wa ta'adin gaske inda dubban mutane suka rigamu gidan gaskiya.