1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola: Saliyo za ta sa dokar hana fita

September 6, 2014

Gwamnatin Saliyo ta ce nan gaba cikin wannan watan za su sanya dokar hana fita ba dare ba rana har tsawon kwanaki uku a wani mataki na dakile yaduwar cutar nan ta Ebola.

https://p.dw.com/p/1D8Cc
Ebola in Liberia (Behandlung im Krankenhaus)
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Abdulai Bayraytay da ke magana da yawun gwamntin ta Saliyo ya ce mahukuntan kasar sun yake hukuncin ware wadanan kawakin ne don baiwa jama'a damar tanadar kayan abinci da isasshen ruwan gabannin fara aikin dokar daga ranar 19 zuwa 21 ga wannan watan.

To sai dai dama ciki kuwa har kungiyar agaji ta likitoci ta Doctors Without Boders sun ce zai yi wa jami'an kiwon lafiya wahalar gaske na su karede fadin kasar da nufin zakulo masu dauke da wannan cuta, lamarin da ya sa ake ganin shirin ba zai yi wani tasirin gaske ba.

Kungiyar ta kara da cewar ko ma da an kai ga gano masu dauke da cutar a bincike gida-gidan da za a gudanar Saliyo ba ta isassun kayan aikin da za ta killace masu dauke da cutar masu tarin yawa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman