ECOWAS ta dage wa Nijar takunkumi
February 24, 2024Talla
ECOWAS ta yanke shawarar dagewa ba tare da bata lokaci ba wasu daga cikin takunkuman da ta kakaba wa Nijar tun bayan kwace mulki a Yamai da gwamnatin soja ta hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a watan Yuli. Za a sake bude iyakokin da sararin samaniya, a cewar sanarwar a karshen babban taron shugabannin kasashen ECOWAS.