1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta nemi Barrow ya zauna a Senegal

January 15, 2017

Senegal ta amsa kirar da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta yi mata na bai wa zababben shugaban kasar Gambiya Adama Barrow mafaka har ranar da za a rantsar da shi a kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/2VpOX
Gambia nach Präsidentschaftswahl - Wahlsieger Adama Barrow
Hoto: Getty Images/AFP/Sellou

Gwamnatin Senegal ta amince wa zababben shugaban Gambiya Adama Barrow ya zauna cikin kasar har lokacin da za a rantsar da shi a ranar 19 ga wannan wata na Janairu. Kanfanin dillanci labaran Senegal APS ya ruwaito cewar kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ce ta mika wannan bukata ga hukumomin Dakar. Dama dai zababben shugaban kasar Gambiya ya isa babban birnin na Senegal bayan ganawa da ya yi da shugabannin ECOWAS ko CEDEAO a daura da taron Mali tsakanin Afirka da Faransa.

Ita dai Gambiya ta fada cikin rikicin siyasa bayan da shugaba mai barin gado Yahya Jammeh ya yi amai ya lashe, inda ya fara amincewa da shan kaye, kafin daga bisani ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa. Baya ga ECOWAS ko CEDEAO, shugabannin kasashe  da dama na Duniya suna matsa wa Jammeh lamba don ya sauka cikin girma da arziki. Sai dai ya ce zai ci gaba da turjewa har sai kotun kolin Gambiya ta yi nazarin karar zabe da ya shigar.