1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: ECOWAS za ta afka wa masu juyin mulki

August 19, 2023

Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta ce ta amince da ranar da za ta tura dakarun ko-ta-kwana domin mayar da Nijar tafarkin dimukuradiyya. Amma sojojin Mali da Burkina Faso sun sha alwashin kai wa sojin Nijar din dauki.

https://p.dw.com/p/4VLa2
Kwamishinan harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro na kungiyar  ECOWAS Abdel-Fatau Musah
Hoto: Richard Eshun Nanaresh/AP Photo/picture alliance

A cikin jawabinsa yayin kammala taron kwanaki biyu na manyan hafsoshin sojin Kungiyar da ya gudana a birnin Accra na kasar Ghana, kwamishinan harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro na kungiyar Abdel-Fatau Musah ya ce, a shirye suke domin ba da umurni a kowane lokaci.

Ya kara da cewa an cimma ranar da za ECOWAS za ta dauki matakin soji a kan sojin Nijar din, sai dai kuma bai bayyana takamaimiyar ranar ba. Kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Afirka ta Yamma ECOWAS na ci gaba da tattauna yadda sojojin Nijar da suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum za su mika mulki da karfin soji, sai dai Musa ya kara da cewa, tattaunawar zaman lafiya ita ce babban abun da kungiyar ta fi so.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da sojojin da ke mulkin kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar suka yi wata ganawa a birnin Yammai a wannan Asabar domin tattauna hanyoyin hadin gwiwa wajen kare Nijar daga harin da kungiyar ECOWAS ke shirin kai mata domin kwace mulki a hannun sojojin da suka hambarar da mulkin shugaba mohamed Bazoum.