ECOWAS na neman sulhu a Nijar
August 25, 2023Jaridar ta ce kamar yadda jagoran Juyin mulkin Abdourahmane Tchiani ya nuna wannan juyin mulkin aiki ne na kishin kasa, in ji shi. Sai dai abin tambaya shi ne shin juyin mulkin zai iya zama alheri ga kasar Nijar? A waje guda dai tuni kasashen Turai da suka hada da Amurka da Jamus suka juya wa sojojin baya. Kasashen na Turai ciki har da Faransa wadda ta yi wa Nijar mulkin mallaka suna da sojoji da ke taimaka wa Nijar ta fannin tsaro da yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel. Jaridar ta kara da cewa a baya, kamar an ci nasara wajen dorewar dimukuradiyya a Afirka to sai dai juyin mulkin na Nijar ya mayar da hannu agogo baya a kasar ta yammacin Afirka inda ba zato ba tsammani sojoji suka kifar da gwamnatin da jama'a suka zaba ta hanyar dimukuradiyya.
ECOWAS ta yi kira da a gaggauta dawo da mulkin Bazoum Mohammed
Jaridar ta yi waiwayen baya inda ta ce a shekarar 2020 sojoji sun hambarar da shugaban kasar Mali. An yi juyin mulki a Guinea a shekarar 2021. Haka kuma an yi juyin mulki a kasar Chadi inda bayan rasuwar shugaba Idriss Deby dansa wanda shi ma soja ne ya karbi ragamar mulki. Haka ma dai Sojoji sun yi juyin mulki a Burkina Faso. Domin taka birki ga juyin mulkin soji a nahiyar, kungiyar raya cigaban Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta yamma Ecowas wadda ke kallon kanta a matsayin jigon daidaita tattalin arziki da siyasa a yankin. ta yi kira da a gaggauta dawo da gwamnatin da aka hambarar ta shugaba Bazoum Mohammed tare da barazanar yin amfani da karfi idan sojojin suka ki bin wannan umarni. To amma shin Ecowas za ta iya kai hari ba tare da samun goyon bayan kasashen na yammacin Afirka ba? A karkashin dokokin kasa da kasa dai, hakan zai zama keta doka kamar yadda Rasha ta yi a Ukraine inda cikin barazana a 2014 Rasha ta mamaye Crimea ba bisa ka'ida ba. A matakin ladabtarwa kungiyar tarayyar Afirka AU ta dakatar da Nijar daga cikinta bayan takunkumin karya tattalin arziki da Ecowas ta kakaba wa kasar. A yanzu dai kungiyar Ecowas na kan yunkuri na kafa runduna mai karfi ta wanzar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
BRICS na son kalubalantar babakeren kasashen yammacin duniya
Jaridar Frankfueter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci ne kan taron kungiyar kasashen BRICS wacce ke son kalubalantar babakeren kasashen yamma ta fuskar tattalin arziki. Jaridar ta ce babu shakka kasashen BRICS sun kunshi kashi 40 cikin dari na al'ummar duniya da kuma kusan kashi hudu na abubuwan da ake fitarwa na tattalin arziki a duniya. Jaridar ta ce ko da yake wasu daga cikin mambobin kasashen kungiyar suna adawa da wasu tsare tsare na yammacin turai amma kawancen yana da rauni saboda mambobin kasashen sun banbanta ta bangarori da dama. Sai dai ana iya cewa kasar Afirka ta kudu wadda ta karbi bakuncin taron, babu shakka ta sami karin daraja. Ya zuwa yanzu, kuri'ar jin ra'ayin jama'a a Cape town, ya nuna an samu karin tuntuba da kuma rarrabuwar kanu akan matsayin shugaba Cyril Ramaphosa akan kasar Rasha wadda ke neman karfin tasiri a kasashen Afirka.