1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EFCC: Binciken 'yan APC ya tayar da kura

May 4, 2017

Jama'a sun soma tsokaci kan matakin gwamnatin Najeriya a yakin da ta ke da cin hanci a tsakanin manyan jiga-jigan 'yan jam’iyar APC mai mulki, inda wasu ke kallon lamarin tamkar da biyu.

https://p.dw.com/p/2cMmi
Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.Hoto: DW/T. Mösch

Na baya-bayan nan dai a cikin binciken na zaman tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwanso da ya samu ziyara ta jami'an 'yan sanda ya zuwa gidan kaninsa garin Madobi da ke jihar Kano da nufin bankado kudade da makamai da ake da tunanin tsohon gwamnan ya boye. Kwankwaso dai na zaman sanatan jam'iyyar APC mai mulki na uku da ya fuskanci ziyara ta jami'an tsaron cikin sabon shiri na bankado kudade da makamai na gwamnatin ta Najeriya.

Nigeria Oppositionspartei APC
Tutar jam'iyya mai mulki ta APC a Tarayyar Najeriya.Hoto: DW/K. Gänsler

Tun kafin shi, dama 'yan sandan sun ziyarci gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje da kuma Sanata Sabo na Kudu daga jihar Jigawa. Wannan abu dai daga dukkan alamu ya harzuka 'yan APC din da suka taka rawa wajen tabbatar da sauyi ga kasar amma kuma ake kallon sauyin na neman wucewa da saninsu. Duk da cewar dai a fadar tsohon gwamnan na Kano 'yan sandan sun kare tare da cin karo da zomaye maimakon akwatunan kudi ko na makamai dai, sabon yanayin da ke zaman manufa ta gwamnatin APC na da  bukatar taka tsan-tsan da ma sanin yakamata a fadar kwankwason.

Nigeria EFCC Bankole in Abuja
Jami'an hukumar EFCC cikin ayyukansu na kama wadanda ake zargiHoto: DW

To sai dai kuma ko bayan 'yan APC din dai, su ma 'yan jam'iyyar PDPD da ke adawa a halin yanzu na taraddadi a fadar, mataimakin shugaban majalisar dattawan Tarrayar ta Najeriya Sanata Ike Ekweremadu da ya ce ana shirin a tura makamai da kudade a gidansa, zargin kuma da hukumar EFCC ta ce ya yi kama da mafarkin rana ga duk wanda ya ke takama da gaskiya cikin harkokinsa. To sai dai kuma a fada ta Kwankwason akwai tsoron yi wuwar rikidewar yakin hancin ya zuwa tsohuwar siyasar gaba, wanda a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakaki na gwamnatin sabon yakin ba shi aboki balle makiyi sai dai kowa tasa ta fishe shi.