EFCC ta gurfanar da Dick Cheney a gaban Ƙuliya
December 8, 2010Talla
A wani abun da ke iya sauya dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, hukumar da ke yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa EFCC, ta gurfanarda tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amuruka Dick Cheney da waɗansu mutane takwas gaban ƙuliya. Ana zarginsu ne da laifin cin hanci da rashawa a kan abin kunyar da ya faru a kampanin Halliburton na Amurka, ko da yake awai jan aiki ga hukumar, na tuso ƙeyar tsohon mataimakin shugaban ƙasar ta Amurka zuwa Najeriya.
Mawallafi: Uwais Idris Abubakar
Edita : Zainab Mohammed Abubakar