1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Erdogan ya cika alkawarinsa kan shigar da Sweden cikin NATO

Mouhamadou Awal Balarabe
October 23, 2023

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya mika wa majalisar dokokjin kasarsa bukatar Sweden na zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO a hukumance, bayan shafe watanni 17 yana adawa da wannan mataki.

https://p.dw.com/p/4XvIX
Shugaba Erdogan ya shafe watanni 17 na adawa da shigar da Sweden cikin NATO
Shugaba Erdogan ya shafe watanni 17 na adawa da shigar da Sweden cikin NATOHoto: Presidential Press Office/REUTERS

Firayiministan kasar Sweden Ulf Kristersson ya yi amfani da kafar X wato Twitter wajen yin maraba da abin da ya danganta da "kyakkyawan labari", inda ya ce rage wa majalisar Turkiyya ta cika musu fatan zama memba a kungiyar tsaro ta NATO. A watan Yuli ne Shugaba Erdogan ya sauka daga kujerar na ki tare sahale wa Sweden ta shiga kungiyar ta kawancen tsaro, inda ya bayyana cewa amincewar za ta dogara ne ga majalisar dokokin Turkiyya idan ta koma bakin aiki bayan hutun bazara.

Karin bayani: Matakan shigar Sweden NATO daga Turkiyya

Mr. Erdogan wanda ya tattauna ta wayar tarho da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg, ya ci gaba da matsa wa Sweden lamba domin ta dauki matakan hana kona Alkur'ani mai tsarki, wanda ya kara dagula alaka a tsakanin kasashen biyu. A daya hannun kuma, Ankara ta soki mahukuntan Sweden kan yadda suke nuna sassauci kan Kurdawa 'yan gwagwarmayar da suka samu mafaka a kasar tare da neman a mika musu da dama daga cikinsu ga Turkiyya.

Karin bayani: NATO na tunanin sama wa kasar Ukraine gurbi

Dama dai Hongari da Turkiyya ne kasashen karshe a cikin mambobin NATO 31 da ba su kai ga amince da zaman Sweden mamba ba.  Idan za a iya tunawa dai, Ankara ta tabbatar da shigar Finland a ranar 30 ga Maris, amma ta hau kujerar na ki game da Stockholm.