Erdogan: 'Yan gudun hijira na bukatar agaji sosai
May 23, 2016An dai tsammaci samar da sauyi kan yadda ake ayyukan tallafin al'umma a yayin wannan taron koli na Istanbul. Sai dai tun kafin wannan rana kungiyoyin agaji irin su MSF ta likitocin kasa da kasa sun bayyana taron a matsayin rufa-rufa ta abin kunya. Shi kuwa a fadarsa Ban Ki- moon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya taron na zuwa ne dan babu zabi duba da halin da al'ummar duniya ke ciki.
Ya ce "Adadin al'umma miliyan 130 na bukatar tallafi don su rayu, mutane da dama an tilastasu barin muhallansu, sun yi hijira da ke zama mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu."
DW ta tambayi Christina Bennett wacce ta yi kimanin shekaru 10 tana aiki da sashin agaji na Majalisar Dinkin Duniya, yanzu kuma take aiki da wata cibiyar kwararru mai bincike ta Overseas Development Institute (ODI) a birnin London, kan yadda ta kalli wannan taro na Turkiya.
Ta ce "Mun yi taron koli kan ci gaba mai dorewa SDG, mun yi kuma kan yadda za a rage hanyoyin da ke kaiwa ga aukuwar bala'o'i, ga kuma yadda muka yi taro kan sauyin yanayi. Don haka kowa ya sani duniya a yau na fama da kalubale da ke bukatar kulawa ta fiskar fannin al'umma."
Bukatar ganin agajin gaggawa a kasa
Shi ma dai mai masaukin baki shugaban kasar ta Turkiya Recep Erdogan wanda kasarsa ke da 'yan gudun hijira da suka haura miliyan biyu musamman daga Siriya, a wajen buden taron jaddada bukata ya yi ta ganin tallafin kasashen a kasa, ba alkawura ba.
Ya ce " ina fatan wannan taro zai kai ga irin bukatar da al'umma ke da ita musamman miliyoyin daruruwa da ke neman yadda za su rayu bayan da suka samu kansu cikin kaka na ka yi."
Kungiyar dai ta ODI ta bada rahoton bincikenta na tsawon shekaru hudu wanda ya nunar da cewa bada tallafin al'umma a duniya tsawon shekaru 25 a ayyukan kungiyoyin masu zaman kansu da MDD bai wuce gyara kujeru ba a cikin katafaren jirgin ruwan da ya tasamma nitsewa a teku, maimakon a samar da karin jiragen ceton al'umma, kammar yadda Bennett ke cewa.
"Tsarin yadda ake tallafin al'umma tsoho ne tun a shekaru 75 da suka wuce ake kansa, a yau idan ka duba bala'oin da ake fiskanta sun banbanta, akwai masu tsauri ta fuskar zamantakewa da sauyin na yanayi, akwai rikici na cikin kasashe inda kungiyoyi ke dauke da makamai, a yau ana amfani da jirage marasa matuka wajen kai farmaki, yadda aka tsara tunkara matsalolin da al'umma ke fiskanta a shekarar 1945 ba su ne ake gani ba a wannan lokaci da al'umma ke fama da tarin matsaloli."
Yayin wannan taro dai manyan masu bada agaji 15 da masu aikin agajin manya15 ana saran su cimma daidaito, yayin da bangaren masu bada agaji za su bada karin kudade, su kuma masu aikin su bayyana daki-daki kan yadda za su yi amfani da kudaden.
Kungiyar likitoci ta MSF dai ta bayyana taron a matsayin na rufa-rufar abin kunya ko ya kungiyoyin masu bincike irin na ODI ke kallon wannan suka anan ma ga Bennett.
Ta ce "akwai matsala, sai dai ina sa ran wannan yunkuri na kungiyar ta MSF zai sanya hankali kowa cikin masu ruwa da tsaki a harkar agaji su kara azama, domin abu ne da ya shafi dukkaninmu, idan muna son taron kolin na tallafin al'umma ya samu nasara, dole a mara bayan kalaman baka da aiyuka, mu kudiri niyar aiki mu cika shi a kan lokaci, ba kawai alkawura ba yadda koda bayan taron za mu ga nasara."
Abin jira a gani na zama yadda taron na kwanaki biyu zai kaya da ma irin taimakon da kasashe da kungiyoyin agajin za su bada.