Al'ummar Tigray na kada kuri'unsu
September 9, 2020Talla
Fraiministan ya ayyanashi a matsayin saba doka, duk da cewar gwamnati ba ta da niyyar martani da jami'an tsaro.
A baya dai an tsara gudanar da zaben yankunan kasar ta Ethiopiya a ranar 29 ga watan Augustan da ya gabata, kafin a dage shi saboda barkewar annobar corona. 'Yan adawa a yankin na Tigray sun zargi Abiy Ahmed da kokarin fadada wa'adinsa na mulki.
Sa-in-sa da Tigray, na daga cikin rigingimun baya-bayannan da fraministan Ethiopiyan ke fuskanta, mutumin da ke fafutukar dinke barakar da ke barazanar wargaza hadin kan kabilun kasar sama da 80.
Tuni dai 'yan siyasar Tigray suka yi gargadin cewar, yunkurin tsayar da kuri'un da aka fara kadawa a zaben na yau, zai fuskanci martanin yaki.