1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar G20 a Riyadh

Zainab Mohammed Abubakar
November 21, 2020

Hukumar gudanarwa da majalisar tarayyar Turai sun bada hujjojinsu na halartar taron kasashe masu cigaban masana'antu na G20 a Saudi Arabiya, duk da adawar majalisar Turan.

https://p.dw.com/p/3leV3
Brüssel EU Sondergipfel Michel von der Leyen
Hoto: Dursun Aydemir/AA/picture-alliance

A watan da ya gabata ne dai, wakilan majalisar Turan suka yi kira ga kungiyar ta EU, da ta kauracewa halartar taron na birnin Riyadh saboda dalilai na kin mutunta hakkin bil Adama a bangaren Saudiyya.

Kudurin da ke zama daya daga cikin suka mafi karfi na siyasa da majalisar Turan ta taba gabatarwa a kan Saudi Arabiyar, na zuwa ne shekaru biyu bayan kisan gillan da aka yi wa fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi.

Kudurin ya yi Allah wadan take hakkin jama'a da mahukuntan Saudiyya ke yi, tare da kira ga shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen da shugaban majalisar kungiyar Charles Michel, da su kauracewa taron.

Sai dai manyan jami'an Turan biyu na halartan taron da ke gudana a yau a birnin Riyadh.