1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Wasu kasashe na da hadarin corona

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 9, 2021

Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta cire Japan da Albaniya da Armeniya da Azarbaijan da Burunai da kuma Sabiya da Yurugai daga cikin kaasashen da ba su da hadari dangane da annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/408Ug
Symbolbild Kontrolle Covid-19 Coronavirus App Flughafen
Wasu kasashe na da hadarin kamuwa da cutar coronavirusHoto: ROBIN UTRECHT/dpa/picture alliance

Hakan na nufin bakin da suka fito daga wadannan kasashe ko kuma mutanen da suka dawo daga hutu, ka iya fuskantar matakan kariya daga yaduwar annobar ta COVID-19 masu tsanani kamar killacewa da kuma gwaje-gwaje. A yanzu haka kasashe 12 ne EU din ta bayyana da cewa ba asu da hadari. Kasashen kuwa sun hadar da Ostireliya da Kanada da Saudiyya da kuma yankunan Hong Kong da Macao na kasar Chaina. Kungiyar ta EU dai na kyale da dama cikin al'ummar kasashe mambobinta da aka yi wa allurar riga-kafi su yi zirga-zirga a tsakani, sai dai duk da haka akwai yiwuwar sanya kwanakin killace kai da suka shafi wacce kasa daga cikin kasashe 27 na EU din suka fito.