1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta karfafa taimakon tsaro ga Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe
July 6, 2023

Kantoman harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrel ya sanar da cewa EU za ta karfafa goyon bayanta na soji ga Jamhuriyar Nijar domin yakar 'yan ta'adda a yankunan da ke kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/4TTfU
Kungiyar Tarayyar Turai ta shafe shekaru tana taimaka wa sojojin NijarHoto: Marou Madougou Issa/DW

 A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar bayan da tattaunawa da shugaba Mohamed Bazoum a birnin Yamai, babban jami'in EU Joseph Borell ya ce Nijar za ta kasance kasa ta farko a Afirka da za ta ci gajiyar irin taimakon domin karfafa sojojin da kayan yaki na zamani, wadanda suka hada da harsasan da jirage masu saukar ungulu ke amfani da su.

Joseph Borell ya kara da cewa EU na tallafa wa Jamhuriyar Nijar saboda yunkurinta na tabbatar da dimokuradiyya da gudanar da shugabanci na gari, baya ga karfin hali da sojojinta ke nunawa don magance matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin Sahel. Mr Borrell zai je Agadez da ke arewacin Nijar don ziyartar ayyukan ba da agajin tsaro wanda EU ke tallafawa.

Ita dai  Jamhuriyar Nijar da ke zama daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, tana fuskantar matsalar 'yan fashi da makami ko kungiyoyin jihadi a shida daga cikin iyakokin ta bakwai da kasashe makwabta.