1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta rage yakar fasakauri a tekun Bahar Rum

Yusuf Bala Nayaya MNA
March 27, 2019

Sai dai aikin dakarun mai lakabin "Operation Sophia" zai ci gaba da aiki ta hanyar amfani da jiragen sama da ma ci gaba da ba da horo ga jami'an da ke kula da iyakar teku a Libiya.

https://p.dw.com/p/3FhjC
Europa Symbolbild Grenzschutzmission "Sophia" rettet weniger Menschen
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Lami

Kungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da jibge dakarun sojan ruwa da ke aikin yaki da masu fataucin mutane a tekun Bahar Rum, matakin da ke zuwa bayan shiga takaddama tsakanin mambobi na kungiyar kamar yadda majiyar ta EU ta fada wa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA.

Sai dai aikin dakarun mai lakabin "Operation Sophia" zai ci gaba da aiki ta hanyar amfani da jiragen sama da ma ci gaba da ba da horo ga jami'an da ke kula da iyakar teku a Libiya.

Idan mambobi na kungiyar ta EU sun ki amincewa da batun dakatar da aiki nan da zuwa sha biyun rana a wannan Laraba da su kalubalanci matakin, idan ba haka ba kuwa dakatarwar za ta ci gaba har tsawon watanni shida.