1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta saka wa Koriya ta Arewa sabbin takunkumai

Gazali Abdou Tasawa
October 10, 2017

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta karkama wa Koriya ta Arewa wasu takunkumin tattalin arziki kan shirinta na nukiliya.

https://p.dw.com/p/2laQ6
Nordkorea Wonsan Pier mit Schiff und Anglern
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Wong Maye-E

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta dauki a wannan Talata wasu sabbin matakai na takunkumin tattalin arziki kan Koriya ta Arewa a wani mataki na aiwatar da kudurin da majalisar dinkin duniya ta dauka a ranar 11 ga watan Satumban da ya gabata a matsayin martani ga gwajin makamin nukiliya da Koriya ta Arewar ta gudanar a farkon watan na Satumba. 

Sabbin matakan da Kungiyar at EU ta dauka sun tanadi haramta wa kamfanonin kasashen Turai sayar wa Koriya ta Arewa da iskar gaz da kuma odar tufafi da yadi daga Koriya ta Arewar zuwa kasashen na Turai, da kuma takaita yawan man fetur da kasashen za su sayar wa wannan kasa. 

Kazalika kasashen na Turai za su dakatar da bayar da lasin aiki ga 'yan Koriya ta Arewa a mazauna Turai da ke basu hurumin shigowa kasashen na Turai da kuma gudanar da aiki, musamman wadanda ake zargin kudaden da suke aikawa gida na iya taimakawa ga abin da suka kira haramtaccen shirin nukiliya. Ana sa ran sabbin matakan za su soma aiki tun a tsakiyar wannan wata na Oktoba